Bisa ga al’adar Masarautar Kano duk shekara cikin bukukuwan Sallah ta kan shirya hawan Sallah domin shagalin bikin Sallar, cikin farin ciki da bin sahun al’ummar musulmi na Duniya da ke yin bikin Sallah.
Haye-hayen bukukuwan Sallah da Sarki mai ci ke jagoranta sun haɗa da hawan Idi da Daushe, Nasarawa, da kuma Hawan Fanisau ko Dorayi a ƙaramar Sallah ko babba.
Al’ummar birnin Kano da kewaye har daga wasu jihohi zuwa ƙasashen waje na haɗuwa a birnin domin sheda hawan, in da sarakuna ke yin kwalliya da hawa dawaki masu kayatarwa da ke jan hankalin masu kallo da shiga iri-iri da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe irin na sarautar gargajiya.
Ba kasafai aka cika ƙin yin hawan ba, to amma a wasu lokuta an sha soke yin hawan saboda dalilai na tsaro ko akasin haka, ko a babbar Sallar bara ma sai da rundunar Ƴansandan jihar Kano ta soke yin hawan saboda dalilan tsaro.
Hawan ƙaramar Sallah na 2024 shine hawa na ƙarshe da aka yi a masarautar ƙarkashin Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero, daga nan ne ɓaraka ta kunno kai, in da gwamnatin mai ci ta Abba Kabir ta sanar da sauke Sarkin Kano na 15 Aminu Ado ta kuma dawo da Sarkin Kano na 14 Muhammadu Sunusi wanda Gwamnan baya Ganduje ya sauke shi a wancan lokacin.
Tun daga lokacin ne ake taƙaddama kan sarautar birnin Kano lamarin da ya ke gaban kotu, tsakanin Sarkin Kano Sunusi da Sarki Aminu ko wa na jin cewa shine Sarki.
Zuwa yanzu taƙaddamar ba ta ƙare ba domin kuwa gashi har ana shirin kammala Azumi watan Ramadan 29 ko 30, in da tini dukkan sarakunan su ka fara shirin hawan Sallar.
Wata takarda da aka yaɗa a kafafen sada zumunta, ta nuna yadda bangaren Sarki Sunusi ya umarci hakiman da ke yi masa biyayya da su shigo birnin Kano domin shirin hawan da kuma zaman fadanci da Sarkin ke yi a kwanaki goman ƙarshe na Azumin watan Ramadan.
Shima ana sa bangaren Sarki Aminu Ado, wasu takardu da su ka dinga yawo a kafafen sun gwada yadda Sarkin ya sanarwa da jami’an tsaro shirinsa na yin hawan.
Ko a cikin makon nan a yayin wani shan ruwa da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya shirya wa sarakunan ya yi umarnin cewa sarakunan su zama cikin shiri su kuma shigo birnin Kano domin gudanar da hawan Sallar.
Rundunar Ƴansandan Kano ta bakin Kwamishinanta Ibrahim Adamu Bakori ya ce za su bayar da duk wani tsaro da ake buƙata a lokacin bukukuwan Sallar ta bana.
Zuwa yanzu tini al’umma su ka fara dasa ayoyin tambaya, shin ta ya ya sarakunan za su iya yin hawa biyu a lokacin bikin Sallah?
Idan kuma Sarki ɗaya ne zai yi wa za a bari wa kuma za a hana?
Shin za ma a yi hawan Sallar ko kuma hana wa za ayi baki ɗaya?