April 18, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Sojojin Najeriya sun sheƙa ƴan bindiga 31 lahira a jihar Katsina.

Dakarun sojojin Najeriya sun kai farmaki kan ƴan bindiga da ke addabar wasu yankunan jihar Katsina, in da suka kashe 31 a hare-hare biyu daban-daban.

Rahotanni sun nuna cewa farmakin farko da sojojin Operation Fansa Yamma suka kai, ya yi sanadin kashe ‘yan bindiga 12 ciki har da wani babban kwamanda da aka fi sani da Dogo, tare da kwace babura guda bakwai.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Maigora da ke ƙaramar hukumar mulkin Faskari, in da ƴan bindiga suka kai hari kuma aka kashe biyar daga cikin su.

Bayan sun sake tattaruwa don kai farmaki na ramuwar gayya, sojoji sun mayar da martani akan su, wanda ya yi sanadin kashe ƙarin ƴan bindiga bakwai.

A wani farmaki daban, rundunar sojojin saman Operation Fansa Yamma ta kai hare-haren bama-bamai a sansanonin ‘yan bindiga da ke cikin dajin Unguwar Goga da ke yankin Ruwan Godiya, ƙaramar hukumar Faskari.

A wannan harin, an lalata sansanoni biyu manya na fitattun shugabannin ‘yan bindiga da suka haɗa da Alhaji Gero da Alhaji Riga, tare da kashe akalla ‘yan bindiga 19.

Daily Trust ta rawaito, bayanai daga majiyoyin tsaro sun nuna cewa dakarun sojoji na ci gaba da matsa ƙaimi, wajen kawar da ‘yan bindiga a yankin Arewa maso Yamma, tare da lalata sansanonin su da hanyoyin samar musu da kayan abinci da makamai.

Haka kuma, majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa an ɗauki matakan sintiri ta sama da ƙasa, don bibiyar ‘yan bindigar da suka tsere da kuma hana su sake haɗuwa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *