Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU, ta sake jaddada kiran a gaggauta biyan albashin mambobinta na watanni hudu da aka hana su albashi.
Shugaban ƙungiyar SSANU Mohammed Ibrahim, ne ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar da ya fitar ranar Lahadi a Abuja, a ƙarshen taron majalisar zartarwa na kasa.
Tun a baya Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayar da umarnin a biya duk albashin malaman da aka hana.
Mista Ibrahim ya ce an kira taron ne domin a magance korafe-korafe da suka haɗa da albashin da ake hana su, da gazawar tsare-tsare da kuma jinkirin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma da mambobinta.
“Muna cikin damuwa har yanzu mambobinmu ba su karbi albashin da ya kamata ba kusan watanni biyu bayan umarnin,” in ji shi.
Ba ƙwace motocin sojoji ƴan bindiga su ka yi ba – Mazauna Zamfara.
Crypto: Kotu ta Aike Wa Gwamnan CBN Sammmaci Don Ya Gurfana A Gaban Ta.
Kotu: An Tsare Ɗan Jarida A Gidan Yari Kan Zargin Ɓata Sunan Gwamnan Kano Abba.
Ya kuma ce wani babban abin da ya dame shi shi ne rashin biyan su alawus-alawus din da aka yi wa kasafin Naira biliyan 50 a shekarar 2023 amma abin ya ci tura.
Ya bukaci gwamnati da ta binciki jinkirin da aka samu tare da sakin kuɗaɗen cikin gaggawa domin hana ci gaba da kawo cikas a fannin ilimi.
Malam Ibrahim ya kuma yi tir da hauhawar farashin kudin karatu na jami’o’i da kuma kudin siyan kayan masarufi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Mutane 86 ne su ka yi ƙorafi a kan Shamsiyya -Yansanda.
-
Murna ta mamaye al’ummar Gaza byan cimma yarjejeniyar tsagaita ta dindindin.
-
Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.
-
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.