TikTok: Kotu Ta Ɗaure Wani Matashi a Gidan Yari Kan Ɓata Sunan Sheikh Qaribullahi Kabara.
Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wata kutun majistiri mai lamba 82 da ke zamanta a ƙaramar hukumar Gwarzo a jihar Kano, ta ɗaure wani matashi mai suna Abba Mika mazaunin garin Getso, a gidan gyaran hali da tarbiyya bayan da ta same shi da laifukan ɓata suna da kuma cin zarafin Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara shugaban Ɗariƙar Qadiriyya na Afirka da gangan a dandalin sada zumunta na TikTok cikin wani bidiyo da ya wallafa a shafin sa.
Tinda farko an yi zargin matashi ya yi wani bidiyo a shafinsa na TikTok inda ya yi kalaman cin mutumci da cin zarafi da bata sunan Sheikh Qaribullahi, ta hanyar nunawa cewa Shehin Malamin yaje garin Getso ƙarƙashin wata gidauniya ta Mu’assatul Kairiyya Sheikh Qaribullahi, inda ya damfare su kuɗaɗe.
Hakan ne yasa wani mutum mai suna Tasi’u Abdullahi Getso, da wasu mutam huɗu suka shigar da ƙorafi ga rundunar ƴan sandan jihar Kano rashen karamar hukumar Gwarzo, daga nan Ƴan Sandan suka kai wanda ake zargin kotu.
A zaman kotun na ranar Alhamis ɗin nan, an karnatawa wanda ake zargin tuhume-tuhumen da ake masa, inda nan take ya amsa laifin sa.
Duk da amsa laifin sa, kotu ta bawa Abba Mika dama ko zai iya gabatar mata da hujjar da zata hana a hukunta shi, amma ya faɗawa kotun cewa bashi da wata hujja, amma dai yana benan kotun ta yi masa sassauci.
La’akari da haka ne dan sanda mai gabatar da ƙara ASP Jon Sanson, ya nemi Kutun da ta yi wa matashin sassauci, sannan ta sanya shi ya koma inda ya yi ɓantancin ya bawa Sheikh Qaribullahi Kabara haƙuri, sannan kuma ya ƙaryata kansa,
Bayan kotun ta samu matashin da laifukan, mai Shari’a Rakiya Muhammad, ta yanke masa hukunci kamar haka, a laifi na farko zai biya tara naira dubu 20 ko zaman gida yari na watanni uku, a laifi na biyu kuwa tarar dubu 25 ko zaman gidan yari na watanni biyu, sannan kotun ta yake masa sati biyu a gidan yari domin jan kunne da kuma gargadinsa, inda kuma kotun ta umarce shi da ya koma inda ya yi ɓantancin ya ƙaryata kansa da kuma bawa Sheikh Qaribullahi Nasiru Kabara haƙuri tare da duk wanda ya ɓatawa.
Ta kuma umarce shi da yasa hannu kan wata tarda da ta hana shi aikata laifi kowane iri har na tsawon shekaru biyar.
Mai shari’a Rakiya Muhammad ta ce laifukan da matashin ya aikata sun saɓawa dokar 129 (8) na ACGL Penal code.
A zantawar Martaba FM da matashin Abba Mika ya ce, ya yi nadama bisa laifin da ya aikata, sannan ya gamsu da duk hukuncin da kotu ta yi masa.