Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano KANSIEC, ta ce ta yi shiri don daukar ma’aikatan wucin gadi kimanin 44,000 domin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da ke tafe.
Za a yi zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin jihar Kano, ne a ranar 30 ga watan Nuwamba, na wannan shekara ta 2024 kamar yadda hukumar zaɓen ta sanar a baya.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren hukumar Anas Muhammad Mustapha, ya ce a zaɓo ma’aikatan wucin gadi a tsanake, “tare da horar da su, da kuma samar da isassun kayan aikin da za su tafiyar da harkokin zaɓe a faɗin ƙananan hukumomin Kano 44, da kuma rumfunan zabe 11,222”.
Mustapha, kuma ce, ana sa ran kimanin masu zaɓe sama da miliyan 6 ne a jihar za su domin kaɗa ƙuri’ar su.
A cewar sanarwar shugaban hukumar Farfesa Sani Lawan Malumfashi, ya ce suna yin shiri gadan-gadan domin tabbatar nasarar aikin “mun riga mun fitar da ka’idojin zabe da jadawalin zaɓe domin bai wa ƴan takara da jam’iyyun siyasa da kuma masu zaɓe isasshen lokaci domin su shirya”.