Kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA reshen Ikeja ta bai wa Gwamnatin Tarayya da Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki, DisCos wa’adin kwanaki bakwai da su janye karin kudin wutar lantarki ko kuma su fuskanci tsatstsaurar shari’a.
Shugaban kungiyar reshen jihar, Seyi Olawunmi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Talata a Legas.
Olawunmi ya bayyana karin kudin wutar lantarki da kusan kashi 300 cikin 100 da cewa ba kawai rashin tunani ba ne har ma da rashin hankali.
Ya ce, umurnin da hukumar kula da wutar lantarki ta kasa, NERC ta bayar kan batun karin kudin wutar, sam babu lura da yanayin tattalin arzikin talakawan Nijeriya a halin yanzu ba.
Ya ce, reshen zai yi duk abinda da ya dace a gaban kotu idan har gwamnatin tarayya da wadanda abin ya shafa suka gaza janye sabon kudin wutar lantarkin da suka bayyana cikin kwanaki bakwai.
Jaridar Leadership
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi martani kan rahoton Amnesty.
-
An yi arangama tsakanin makiyaya da manoma a jihar Gombe.
-
Matuƙa Adaidaita Sahu za su dawo biyan haraji a Kano.
-
Emefiele ne ya mallaki unguwa mai gidaje 753 da EFCC ta ƙwace a Abuja.
-
Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta tseratar da ran mutum 4 a cikin watan Nuwamba 3 sun rasu.