Rahotanni a jihar Revers na cewa, Ƴansanda sun kama wasu mutum 16 da zargin kisan wata sufeton ‘yarsanda a ƙaramar hukumar Khana da ke jihar.
BBC Hausa ta rawaito cewa, lamarin ya faru ne a ranar 25 ga watan Afrilu lokacin da ‘yarsandan mai suna Christiana Erekere ke bakin aiki a ofishin ‘yansanda na Bori.
Wata sanarwa daga mai magana da yawun rundunar, Grace Iringe-Koko, ta ce wasu mutane ne da aka tare domin duba abin hawansu suka halaka jami’ar.
“Bayan kammala duba abin hawan nasu ne aka nemi su tafi, amma sai suka ƙi kuma suka rufe titin gaba ɗaya, inda suka yi zargin cewa matar ta naɗi fuskokinsu a waya,” in ji sanarwar.
“Bayan yunƙurinsu na ƙwace wayar daga hannunta ya gaza, sai suka kai mata hari inda suka jefe ta da duwatsu. Dukan da suka yi mata ya sa sufeton ta sume kuma ta rasu bayan kai ta asibiti.”
Ta ƙara da cewa tuni rundunar ‘yansandan jihar ta miƙa ta’aziyyarta ga iyalin sufeton da kuma abokan aikinta.