Labarai
Trending

Wani Harin Ƴan Bindiga A Jihar Enugu Ya Yi Sandiyar Mutuwar Mutum 4.

Gwamnan jihar Enugu, Dr Peter Mbah, ya bayyana harin na baya-bayan nan da ya yi sanadin mutuwar mutane hudu a Nimbo a matsayin abin da gwamnatinsa ba za ta amince da shi ba, inda ya sha alwashin zakulo wadanda suka kai harin.

Ya bayyana harin a matsayin abin takaici ga daukacin jihar, inda ya bada tabbacin gwamnatinsa za ta hada kai da al’umma da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro domin karfafa tsaro ba a Nimbo kadai ba har ma da karamar hukumar Uzo Uwani baki daya.

Hakan ya faru ne a daidai lokacin da al’ummar yankin Nimbo suka yi kira da a kara karfafa masu kare gandun daji da kuma kula da unguwanni, inda suka jaddada cewa a ko da yaushe maharan su na fitowa ne daga jihohin da ke makwabtaka da su, suna cin gajiyar nesantar al’ummarsu.

Mbah ya fusata ya yi magana ne a wata ziyara da ya kai al’ummar Nimbo ranar Litinin, tare da rakiyar Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Kanayo Uzuegbu; Daraktar Hukumar Tsaro ta Jiha, Theresa Egbunu; Kwamandan Garrison, shiyya ta 82, sojojin Najeriya, Enugu, Birgediya Janar Murtala Abu; da kuma Ko’odinetan kula da dajin na jihar Enugu, Matthew Obodoechi.

“Gwamnan yace bari in tabbatar muku cewa ya isa haka, ba na jin cewa za mu bari a yi a cigaba da yin irin wannan ayyukan kuma mu zuba ido.

“Ba na jin cewa a gaskiya muna da wani dalili na wanzuwa a matsayin gwamnati idan ba za mu iya ba da tabbacin tsaron lafiyar jama’armu ba saboda babban manufar gwamnati ita ce tabbatar da tsaro da jin dadin ‘yan kasa. Dole ne a kawo karshen yanayin da mutanenmu za su kwanta barci da idanunsu biyu. Kuma dole ne a kawo karshen nan take.”

Gwamna Mbah, wanda tun da farko ya kai ziyara tare da jajantawa iyalan da suka rasu, ya yi alkawarin yin aiki da shawarwari da kuma bukatunsu na wakilci a gwamnati da kuma karfafa matakan tsaron yankinsu.

“Mun saurare ku kan batutuwan da kuka gabatar na tabbatar da cewa mutanen Nimbo sun shiga cikin gwamnati, za mu duba yiwuwar hakan, sakon ku yazo,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button