Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa bincike na farko da ayyukan da suka biyo bayan hare-hare na baya-bayan nan da aka kai wa wasu al’ummomi a jihar Filato, sun kai ga cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan mutane a karamar hukumar Bokkos ta jihar.
Wani jawabi da jami’in hulda da jama’a na rundunar ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar da yammacin ranar Laraba, ya ce wadanda ake zargin suna taimakawa a binciken da ake ci gaba da gudanarwa.
Ya bayyana cewa Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya tana yin kokari sosai wajen gano dalilan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane fiye da 50 a safiyar ranar Litinin, da kuma gano da kama sauran masu hannu a kisan.
ACP Adejobi ya kara da cewa, a ziyarar da Sufeto-Janar na ‘Yan Sanda ya kai jihar a ranar Talata, ya umurci Mataimakin Sufeto-Janar mai kula da Ayyuka DIG Kwazhi Dali Yakubu, da ya jagoranci ayukkan da kuma kwantar da tarzoma. “DIG din, bisa ga wannan umarni, ya jagoranci tawagar ‘yan sanda a aikin sa ido ta sama a yankunan Bassa da Bokos, kuma yanzu haka yana ganawa da masu ruwa da tsaki a yankunan da abin ya shafa don tabbatar musu da kasancewar ‘yan sanda a wuraren tare da gina kwarin gwiwa.”
Ya kara da ceea “Bayan bitar lamarin, IGP ya bayar da umarnin gaggauta tura karin jami’an ‘yan sanda da kayan aiki zuwa jahar Filato. Wadannan karin jami’ai za su taimaka wajen hanzarta amsawa da sintiri a wuraren da ke da haɗari, da tattara bayanai masu mahimmanci da kuma magance barazanar da ka iya tasowa. Tawagar ‘yan sanda karkashin jagorancin DIG mai kula da Ayukka ta fara tantancewa don tsara yadda za a tura karin kayan aiki na musamman.”
A halin da ake ciki kuma IGP Kayode Egbetokun ya yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a jihar Filato, bayan ziyarar da ya kai jihar a ranar Talata, 15 ga watan Afrilu 2025.
Jawabin ya ce, IGP din ya nuna takaicin sa matuka7 game da asarar rayukka, inda ya bayyana wannan danyen aiki a matsayin abin kyama da kuma babbar barazana kan zaman lafiya da tsaron kasa.
Sufeto janar na rundunar yan sandan ya tabbatar wa mazauna jihar Filato cewa Rundunar ‘Yan Sanda za ta ci gaba da kokari, wajen dawo da zaman lafiya da doka, da hana ci gaba da aikata tashin hankali a jihar.