Labarai

An Kama Mutane 6 Da Su Ka Yi Zanga-zangar Adawa Da Natanyahu A Isra'ila.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo da Firdausi Ibrahim Bakondi

Wasu rahotanni daga ƙasar Isra’ila na cewa, ƴan sanda sun kama wasu mutane 6 a lokacin da suke gudanar da wata zanga-zanga a kofar gidan Firayim Minista Benjamin Netanyahu da ke Caesarea a gabar tekun Isra’ila.

Masu zanga-zangar sun bukaci firaministan da yayi murabus, kan zargin da suke masa na gazawar da ta kai ga harin Hamas a ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.

Rahoton ya bayyana cewa ana sa ran, nan gaba za a gudanar da wata gagarumar zanga-zanga a garin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button