Labarai

Kotu ta bada umurnin dawo da motoci 50 da tsohon Gwamnan Zamfara ya deba

Kotun tayi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya shigar kan mallakar motocin

 

Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Jihar Sokoto, ta yi watsi da karar da tsohon gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle ya shigar kan mallakar wasu motoci kusan 50 da gwamnatin jihar ta ce mallakinta ne.

Idan ba a manta ba a watan Yuni ne rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta kai samame gidajen tsohon Gwamna Matawalle inda suka kwashe wasu daga cikin motocin a lokacin da yake barin kujerar gwamnan jihar a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Litinin, ta ce, reshen babbar kotun tarayya da ke Sokoto ta yi watsi da ikirarin da Matawalle ya yi na mallakar motocin gidan gwamnati.

A cewar sanarwar, tsohon gwamnan da mukarrabansa sun kwashe dukkanin motocin gwamnatin jihar. Ba su bar wa Gwamnati mai ci komai ba.

Jaridar leadership

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button