Labarai
Trending

An Yakenwa Wasu Mutum Biyu Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai A Jigawa Bayan Samunsu Da Laifin Yin Luwadi Da Wasu Yara.

Wata babbar kotun jihar Jigawa da ke zama a Dutse karkashin jagorancin Mai shari’a Muhammad Abubakar Sambo ta yanke wa Isah Haruna hukuncin ɗaurin rai-da-rai bayan samunsa da laifin yin luwaɗi.

An gurfanar da wanda ake tuhumar ne ranar 2 ga watan Mayun 2023, bisa zargin aikata fyaɗe, lamarin da ya saɓa wa sashe na 3 na dokar hana cin zarafin lalata ta (VAPP) a jihar Jigawa 2021.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a ranar 10 ga watan Yunin 2022, wanda aka yanke wa hukuncin ya yaudari wani yaro ɗan shekara 14 a wani kanti da ke Gwaram Sabuwa, a karamar hukumar Gwaram a jihar Jigawa, inda ya yi luwaɗi da shi.

Lauyan mai shigar da ƙara, Sunusi Sani, ya gabatar da shaidu biyar a kan wanda ake kara, shi kuma wanda ake kara ya bayar da shaida don kare kansa.

Alkali mai yanke hukunci, ya bayyana cewa masu gabatar da ƙara sun gabatar da dukkan hujjoji da suka nuna cewa wanda ake ƙara ya aikata luwaɗi, inda ya yanke wa Isa Haruna hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

A wani hukunci kuma, babbar kotu mai lamba 6 da ke zamanta a Birnin Kudu a karkashin Mai shari’a Musa Ubale, ta samu wani Ibrahim Sani da ke kauyen Kiyako na karamar hukumar Birnin Kudu da laifin luwadi da yara, inda ta yanke masa hukuncin ɗaurin rai-da-rai.

An gurfanar da wanda ake tuhumar ne a gaban kotu, bisa tuhuma shida da suka haɗa da luwadi.

Ana zarginsa da yin luwaɗi da wasu yara maza shida masu shekaru tsakanin 11 zuwa 16, laifin kuma da ya saɓa wa sashe na 284 (1) na kundin laifuka wanda aka yi wa gyara na 2014.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button