Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027 - Martaba FM APC ta ƙaryatajita-jitar sauya Shettima a matsayin Mataimakin Shugaban kasa a 2027 - Martaba FM

Jam’iyyar APC, ta musanta rade-radin da ke cewa akwai sabani tsakanin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakinsa, Kashim Shettima, inda ta yi watsi da zancen cewa Tinubu na shirin sauya mataimakinsa gabanin zaben 2027.

Da ya ke zantawa da Daily Trust a jiya Alhamis , Daraktan Yada Labarai na APC, Alhaji Bala Ibrahim, ya ce wadannan rahotanni basu da tushe balle makama.

“Wannan jita-jita ce kawai maras tushe. Wadannan maganganu ne da bai kamata a dauke su da muhimmanci ba,” in ji shi.

“Ko da ace, a wani dalili, shugaba yana da niyyar sauya mataimakin sa, ba zai iya yin hakan shi kadai ba. Wajibi ne a tattauna da manyan jiga-jigan jam’iyya kafin daukar irin wannan mataki,” in ji Bala Ibrahim.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *