Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
CBN ya ƙaryata fitar da takardun kuɗi ƴan dubu 5 da dubu 10 - Martaba FM CBN ya ƙaryata fitar da takardun kuɗi ƴan dubu 5 da dubu 10 - Martaba FM

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya musanta fitar da wata takarda, da ke sanar da samar da sabbin takardun kudi na N5,000 da N10,000.

Takardar da ake cewa CBN ya fitar, wadda ta yadu sosai a kafar sadarwar WhatsApp da Facebook, an karyata ta ne ta hannun babban bankin a cikin wata sanarwa da aka fitar, ta shafin sa na X (wanda a da ake kira Twitter).

Takardar bugin da aka jingina wa CBN ta yi ikirarin cewa: “Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da shigowar sabbin nau’ikkan takardun kudi guda biyu da suka hada da N5,000 da N10,000, a matsayin wani bangare na kokarin saukaka hada-hadar kudi da inganta sarrafa kudaden kasa.”

Sai dai babban bankin ya musanta wannan ikirari, yana mai bayyana shi a matsayin karya.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *