Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
A kalla yara kanana 19 ne suka rasu sanadiyyar kamuwa da cutar Kyanda a karamar hukumar Mubi, dake Jihar Adamawa.
Kwamishinan lafiya na jihar Felix Tangwami ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN a Mubi ranar Asabar cewa sama da yara 200 ne suka kamu da cutar a karamar hukumar.
Ya ce an soma samun labarin barkewar cutar ce a garin Yola, inda cikin gaggawa aka tura jami’an lafiya da magunguna domin a taro cutar kada ta yi ɓarkewar da ba za a iya shawo kansa da wuri ba.
Ya kuma ba da tabbacin cewa za a mika yaran da suka kamu da cutar zuwa snyan asibitocin jihar domin a basu kulawa.
Premium Times ta ruwaito cewa Kwamishinan ya ce tawagar likitocin za su kuma nausa zuwa karamar hukumar Gombi inda aka sake samun bullar cutar.
A karshe Tangwami ya dora laifin kin kai yara asibiti a yi wa ‘ya’ya rigakafin citar tun farko ne yi sanadiyar samun ɓarkewar cutar a yankunan jihar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Za Mu Yi Ƙoƙarin Rage Kuɗin Aikin Hajjin Bana – NAHCON.
-
CEFTPI reveals best Nigerian Govt agency in transparency, integrity
-
Gwamnatin Tarayya ba za ta saka tallafi a kuɗin aikin Hajjin 2025 ba,-NAHCON.
-
Ƙungiyar Hezbollah Ta Harba Rokoki Kan Runbun Jiyar Makaman Isra’ila A Tsakar Daren Jiya.
-
Babban Sifeton Ƴansanda Ya Umarci Jami’ansa Su Janye Daga Sakatariyar Ƙananan Hukumomin Jihar Rivers.