Daga Suleman Ibrahim Modibbo
A ranar Asabar ɗin da ta gabata ce wani labari ya yaɗu kamar wutar daji a kafafen sada zumunta cewa, wanda aka rawaito Mataimakin Gwamnan jihar Bauchi Auwal Jatau, ya mari ministan shugaban Najeriya Tinubu wato Ministan Harkokin Waje Yusuf Tuggar, a yayin da wata ta kaƙaddama ta barke tsakanin Gwamnan jihar Bauchi da ministan a wajen ɗaurin auren ƴar tsohon gwamnan Bauchi Mohammed Abubakar, da kuma naɗa shi sarautar a fadar sarki Bauchi
Labarin ya yaɗu sosai kuma ya jawo ana ta tabka muhawara da ce-ce-ku-ce kan gaskiyar an marin ko ba a yi ba.
To shin da gaske ne Mataimakin Gwamnan ya mari Ministan?
Zuwa yanzu dai Mataimakin Gwamnan Bauchi Auwal Jatau, ya ƙaryata zargin yin marin Ministan.
Da ya ke magana da manema labarai a Bauchi a birnin Bauchi, Sakataren Watsa Labarai na Mataimakin Gwamnan Muslim Lawal, ya ce zargin ƙarya ne tare da jaddada cewa mataimakin gwamna ba zai taɓa aikata haka ba.
Shin da gaske ne an yi marin? “A’a, a’a, ya ya za a ce mataimakin gwamna ya mari minista? Ban yi tunanin irin haka na iya faruwa a Bauchi ba, domin na san ubangidana shugaba ne nagari kuma ba zai taɓa marin wani minista ba”, in Muslum.
Shima ana nasa ɓangaren ɗan Ministan Harkokin Waje na Najeriya Yusuf Tuggar wato Adam Tuggar, ya karyata rahotannin da ke cewa, Mataimakin Gwamnan Auwal Jatau ya mari mahaifin sa.
Sai dai kuma ya soki ɗan Gwamnan jihar Bauchi Shamsuddeen Bala Mohammed, in da ya yi zargin sa da yada ƙarya.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafin sa na Facebook a ranar Asabar, Adam Tuggar ya bayyana cewa bai taɓa shiga muhawarar siyasa a kafafen sada zumunta ba.
Adam Tugga ya ce “yin irin wannan yaɗa jita-jita maras tushe ya tabbatar mini cewa bai canza ba. Ban yi mamaki ba, domin ya taɓa zagin manyan mutane kamar Atiku Abubakar, kawai don suna da bambancin ra’ayin siyasa da mahaifin sa.”
Adam ya ce abin da Shamsuddeen Bala ya yi, na zagin Tuggar, ba dai-dai ba ne kuma rashin kunya ne.
Ya ci gaba da cewa “Game da batun da ake ta yayatawa yanzu, zan iya cewa ko da labarin na karya a ce gaskiya ne cewa mahaifinka ne ya mari Amb. Tuggar, da sai ya koma gida da baki da hanci sun fashe da jini, balle kuma wani mataimakin gwamna mara ƙarfi irin Jatau.
Ministan Harkokin Wajen Najeriya Yusuf Tugga, dai wasu na hasashen zai yi takarar Gwamna ne a Bauchi shekarar 2027 abin da wasu ke ganin zai kawo zafin siyasa tsakaninsa da Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad, wanda ke cin zangonsa na ƙarshe a mulki bayan an zaɓe shi sau biyu.
Ko a watan Nunairun farkon shekarar 2025 sai da aka samun sai-in-sa mai zafi a kafafen yaɗa labarai tsakin Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, da Ministan Harkokin Wajen Najeriya, Yusuf Maitama Tuggar, kan batun sabon kudirin haraji na shugaba Tinubu.