Kasuwanci
Trending

Dala Ta Karye: "Naira 980 Mu Ke Siyan Dala Yanzu- Ƴan canji.

Daga Auwal Kabir Sarari

Kungiyar yan canji ta ƙasa (ABCON) ta bayyana cewa yanzu yan canji (BDC), na siyan dala a kan N980/$ a kasuwar bayan fage ta hada-hadar kuɗaɗen waje, inda su ke sayar da ita kan N1,020/$.

Shugaban ƙungiyar ta ABCON, Aminu Gwadebe ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake gabatar da wani shiri a gidan Talabijin na Channels, mai taken “Business Incorporated”, inda ya bayyana cewa Naira ta kara daraja fiye da yadda ake tsammani idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Gwadebe ya yabawa gwamnati da Babban Bankin Ƙasa, CBN, bisa kokarin da suka yi ya zuwa yanzu, inda ya ce wannan ne karo na farko a cikin shekaru 15 da suka gabata da farashin dala a kasuwar bayan fage ya yi kasa da farashin gwamnati.

Ya kara da cewa yanzu an samu kwanciyar hankali a kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje saboda an daƙile hasashe, wanda ya kasance daya daga cikin abubuwan da ke kawo tabarbarewar kasuwar.

‘’Akwai kwarin guiwa, mun ga yadda aka yi wa asusun ajiyar kudi na babban bankin kasa rajista, kuma mun ga yadda su ma suka yi gyara yadda ake tafiyar da kudaden kasashen waje.

“Yanzu haka muna da tarin kudaden da ake aikewa da su kasashen waje saboda dimbin manufofin babban bankin kasar da suka yi kokarin daidaita yadda kudaden shigar su ke shigowa duk da cewa akwai gibi da yawa da ba sa zuwa wanda har yanzu ba a samu waje ba a cikin kasuwar hada-hadar kuɗaɗen waje ga mazauna kasashen wajen .”

Daily Nigerian Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button