Daga Auwal Kabir Sarari
A Najeriya babbar jam’iyyar adawa ta PDP za ta gudanar da taron majalisar zartarwarta na kasa a Abuja, ranar Alhamis.
Ana sa ran a lokacin taron za a tattauna batun shugabancin jam’iyyar, wanda ya jima yana hannun riko, da dimbin matsalolin da suka dabaibaye jam’iyyar, da kuma kuma tattauna shawarwari kan yadda za a ciyar da ita gaba.
BBC Hausa ta ce, babban taron zai kasance ne yayin da wani rikicin cikin gida ya turnuke a cikin jam’iyyar.
Ana kuma sa ran zai sami halartar kusoshin jam’iyyar daga sassa daban-daban na kasar.