April 18, 2025

EFCC ta gurfanar da wasu mutum biyu kan zargin damfara da sunan A’A Rano

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da wasu mutane biyu a gaban Babbar Kotun jihar Kano, bisa zargin damfarar wani dan kasuwa zunzurutun kudi har Naira miliyan goma sha biyu.

Waɗanda aka gurfanar din su ne Sulaiman Inuwa Zakiru da Aliyu Ahmad, inda ake zargin su da yin karya, da sunan fitaccen attajirin dan kasuwar man fetur A.A. Rano.

An gurfanar da su a gaban Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu kan tuhume-tuhume guda biyu, da suka shafi hada baki da kuma karbar kudi ta hanyar yaudara.

EFCC ta bayyana cewa Waɗanda ake zargin sun yaudari wanda suka damfara, ta hanyar bayyana kansu a matsayin wakilan kamfanin A.A. Rano Oil and Gas Limited.

Daya daga cikin su ya shaida wa wanda ya shigar da kara cewa, Alhaji Rano zai tuntube shi bayan wata ziyarar da aka shirya.

Daga baya wani ya kira wanda aka damfara a waya yana ikirarin shi ne hamshakin da kasuwar man fetur, yana kuma tayin sayar masa da man fetur na Naira miliyan 12.

An umurci dan kasuwar da ya tura kudin zuwa wasu asusun banki guda biyu da ke dauke da sunaye “A.A Yansamary General Enterprise” da kuma “Zahda General Enterprise,” Waɗanda duka ake zargin suna da alaka da Waɗanda ake tuhuma.

Dan kasuwar ya fara shakkar lamarin bayan ya kammala mu’amalar, inda daga bisani ya gana da Alhaji A.A. Rano na gaskiya, wanda ya musanta sanin komai dangane da wannan ciniki.

Dukkan wadanda ake tuhuma sun musanta laifin da ake zargin su da shi.

Lauyan masu kara Zarami Mohammed, ya roki kotu da ta bayar da umarnin tsare su a gidan gyaran hali, sannan ya nemi kotun da ta sanya ranar fara shari’a.

Mai Shari’a Aliyu ta amince da bukatar sannan ta dage ci gaban sauraren shari’ar har zuwa ranar 22 ga watan Mayu 2025.

An umarci a ci gaba da tsare wadanda ake zargi har sai lokacin da sauraron karar zai fara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *