Labarai

Gidauniyar OVPCF Ta Tube Shugabanta Na Bauchi, Tare Da Sallamarsa Baki Ɗaya.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Gidauniyar da ke tallafawa Marayu da Marasa Galihuta Orphans and Vulnerable Populations Care Foundation, a jihar Bauchi ta sallami shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Bauchi Umar Aliyu Saraki, daga gidauniyar, bisa zargin samun sa, saɓa dokokin aiki.

Cikin wata sanarwa da Ukasha Idris Ilela, mai ɗauke da sa hannun mai magana da yawun gidauniyar Shugaban gidauniyar AmbasadaKhalifa Sani Abdullahi, ta ce korar tasa ta biyo bayan binciken da gidauniyar ta yi, inda ta same shi da saɓawa dokokin ƙungiyar.

“An same shi da aikata manyan laifuka biyar ciki da saɓa dokokin ƙungiyar kamar, da gaza miƙa bayanai game da ayyukansa, ga kamar yadda doka ta tanada”, in ji sanarwar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button