Labarai
Trending

A Safiyar Juma'ar An Kashe Mutum 109 A Gaza Bayan Ƙarewar Wa'adin Tsagaita Wuta.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Ma’aikatar lafiya ta Gaza da ke karkashin ikon Hamas ta ce an kashe mutum 109 tun bayan karewar wa’adin tsagaita wuta na wucin gadi a safiyar Juma’a.

Ta kara da cewa an kuma jikkata daruruwan mutane.

Zuwa yanzu dai an kashe mutane sama da 14,800 a cikinsu har da yara kimanin 6,000, tun bayan hare-haren da Isra’ila ta fara kai wa Gaza don ruguza Hamas, wadda ta kaddamar da mummunan harin 7 ga watan Oktoba a kan Isra’ila.

An tsagaita wuta a Gaza ne domin shigar da kayan agaji da kuma kwashe marasa lafiya, a inda rikicin yafi kamari.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button