Notice: Constant DISALLOW_FILE_EDIT already defined in /home/martabaf/public_html/wp-config.php on line 98
Gwamnan Jigawa Namadi ya ƙaddamar da Kwamitin Tsare-Tsare na Shirin Tallafa wa Mata - Martaba FM Gwamnan Jigawa Namadi ya ƙaddamar da Kwamitin Tsare-Tsare na Shirin Tallafa wa Mata - Martaba FM

Daga Sadik Muhammad

Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya kaddamar da Kwamitin Tsare-Tsare na Hada-Hadar Sassa daban-daban domin kula da aiwatar da shirin Nigeria for Women Programme (NFWP) — wani shiri ne da Bankin Duniya ke tallafawa tare da hadin gwiwar Gwamnatin Tarayya.

Martaba FM Online ta ruwaito cewa bikin kaddamarwar ya gudana ne a dakin taro na fadar gwamnatin jihar da ke Dutse a ranar Litinin.

A jawabinsa yayin taron, Gwamna Namadi ya bayyana cewa shirin ya yi daidai da kudirin gwamnatinsa na bunkasa rayuwar mata da habaka tattalin arzikinsu.

“Shirin Nigeria for Women na da nufin inganta rayuwar mata da ci gaban zamantakewarsu. Yana daidai da burin gwamnatina na aiwatar da shirye-shiryen da za su karya tangarorin da ke hana cigaban mata tare da gina musu tubalin habakar tattalin arziki,” in ji Gwamnan.

Kwamitin zai kasance a karkashin jagorancin Kwamishinar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma, Hajiya Hadiza Abdulwahab. Mambobin kwamitin sun hada da kwamishinoni daga ma’aikatun Kudi; Tsare-Tsare da Tattalin Arziki; Lafiya; Noma; Ilimi; Albarkatun Ruwa; da Harkokin Kananan Hukumomi. Babban Sakatare na Ma’aikatar Harkokin Mata zai kasance a matsayin sakatare.

Ayyukan kwamitin sun hada da tantancewa da amincewa da tsare-tsaren aiki da kasafin kudi, hada kai tsakanin hukumomi, tabbatar da hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki, da kuma goyon bayan kungiyoyin mata da na hadin gwiwa.

Gwamna Namadi ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa shirin zai taimaka wajen habaka koyon sana’o’i, kasuwanci, da kuma dogaro da kai ga mata a jihar.

“Muna da kudirin gina muhallin da zai bai wa mata damar inganta rayuwarsu ta tattalin arziki ta hanyar wannan shirin,” in ji shi.

A nata jawabin, Kwamishinar Harkokin Mata kuma shugabar kwamitin, Hajiya Hadiza Abdulwahab, ta gode wa Gwamnan bisa amincewar da ya yi da su, tare da alƙawarin cewa za su yi duk mai yiwuwa domin cimma nasarar shirin.

By Moddibo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *