December 11, 2024

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Gwamnatin Najeriya za ta kammala gyaran matatar mai ta Kaduna zuwa ƙarshen Disamban 2024.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.

Kamfanin man fetur na Najeriya ya bayar da kwangilar gyara matatar man fetur da ta ke jihar Kaduna, wadda ake sa ran aikin zan kammala a watan Disamba na wannan shekara ta 2024.

DCL Hausa, mai yaɗa labarai ta internet ta rawaito, manajan daraktan matatar mai ta jihar Kaduna Dr. Mustafa Sugungun, ya ce, ana sa ran kammala gyaran da ake yi wa matatar ta Kaduna zuwa karshen shekararnan ta 2024.

Babban manajan wanda ya samu wakilcin manajan sashen ayyuka na matatar Mista Emmanuel Ajiboye, ya bayyana hakan a wajen ktaddamar da aikin gyaran wata makaranta da kamfanin ya yi, ya ce idan aka kammala gyaran matatar za ta samar da ayyukan yi, bunƙasa kasuwanci da ƙananan sana’o’i a yankin.

Tsadar Rayuwa: Ba Da Daɗewa Ba Abubuwa Za Su Yi Kyau -Gwamnatin Najeriya.

Hukumar EFCC ta ba wa jami’anta umarnin bincikar gwamnonin da ke kan mulki.

Me ganawar Gwamnan Gombe da Shugaban NNPCL ta ƙunsa?

Jaridar ta kuma rawaito an bayar da gyaran matatar ne a kan kuɗi Dala miliyan 741 ga wani kamfani na ƙasar Koriya ta Kudu mai suna Daewoo Engineering & Construction.

A halin yanzu dai yan Najeriya na ci gaba da shan mai da tsada tin bayan janye tallafin Man Fetur da gwamnatin Tinubu ta yi, masana harkar mai na cewa gyara matatar zai taimaka wajen rage wahalar da ake sha wajen siyen man fetur a wasu lokutan a Arewacin Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *