Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da sabbin ayyuka da gyare-gyare a fannonin tituna, asibitoci, wutar lantarki da aikin noma da suka kai darajar Naira biliyan 750 a faɗin Najeriya.
Ministan Ayyuka, Sanata Dave Umahi, ya ce an amince da gyaran hanyoyi kamar:
Akure zuwa Ado-Ekiti (N19.4bn)
Sokoto–Zamfara–Kaduna (N105bn)
Maiduguri–Monguno (N21bn)
Enugu–Onitsha (N150bn)
Benin–Shagamu–Ore (N187bn)
An kuma amince da gina flyover a Abakaliki (N25bn) da wasu hanyoyi a Ogun da Abia States.
A bangaren lafiya, an amince da:
Sauya asibitin FMC Makurdi zuwa wurin dindindin a Apir, Benue
Shirye-shiryen kare lafiyar jama’a daga cututtuka kamar kwalara
A bangaren wutar lantarki, an kafa National Electricity Policy don gyaran layin samar da lantarki da shigar da makamashi mai tsafta.
Haka zalika, gwamnatin tarayya ta amince da gyaran dam da aikin ban ruwa a Kano da Maiduguri, da nufin bunkasa noman rani da kare ambaliya.
Waɗannan matakai na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.