Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Wasu rahotanni sun ce, Hamas ta ce aƙalla mutum 55 ne suka mutu sakamakon hare-hare ta sama da Isra’ila ta ƙaddamar zuwa Gaza cikin dare, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
Ƙungiyar Ta ce fiye da gidaje 30 ne suka rushe a lokacin hare-haren.
Hakan na zuwa ne bayan da mai magana da yawun sojojin Isra’ila ya ce hare-hare ta sama a Zirin Gaza za su taimaka wa dakarunta da ke ƙasa, wajen tsara ƙaddamar da hare-hare.
Daniel Hagari, ya ce hare-haren za su taimaka wa Isra’ila rage wa dakarunta da ke ƙasa hatsari, wadanda ke jibge a kusa da kan iyaka.
Ya kuma yi kira ga fararen hular Falasdinawa da ke Gaza su ci gaba da ƙaura zuwa kudancin yankin, musamman waɗande ke zaune a birnin Gaza, domin kare lafiyarsu.
BBC ta ce, Isara’ila ta kuma kai wasu ƙarin munanan hare-hare ta sama zuwa Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye.
Inda hari na baya-bayan nan ya faɗa kan wani masallaci a Jenin, wanda sojoin Isra’ila suka zarga da zama ‘cibiyar ‘yan ta’adda”.
Isra’ila na ci gaba da kai hare-hare a Gaza ne tun bayan da ƙungiyar Hamas ta kai mata hari a ranar 7 ga watan Oktoba da muke ciki.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Ƴansanda Sun Kama Wani Ɗan Kasar Aljeriya Da Bindigu A Zamfara.
-
Akwai Bindigogin AK47 Guda Dubu 60 A Sansanonin Ƴan Bindiga Ɗari 120 Cikin Jihohin Arewa Masu Yamma,-Rahoto.
-
Wani Babban Kwamandan Sojin Isra’ila Ya Baƙunci Lahira A Gaza.
-
An Sake Kama Wani Mutum Da Bindigogi A Yayin Da Trump Ke Yaƙin Neman Zaɓe.
-
Mutum Sama Da 20 Sun Mutu A Wani Harin Da Sojoji Su Ka Kai Kasuwa A Sudan.