April 18, 2025

Jami’an tsaro sun cafke masu garkuwa da mutane a jihar Filato.

Jami’an tsaro sun kama wasu masu garkuwa da mutane da ke aikata laifi a karamar hukumar Qua’an Pan ta jihar Plateau.

Shugaban karamar hukumar mulkin Qua’an Pan Christopher Manship, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai cikin wata sanarwa da babban mai ba shi shawara na musamman kan harkokin watsa labarai Danaan Sylvanus ya sanyawa hannu.

Ya kuma tabbatar da cewa an kwato Naira miliyan biyu da dubu dari biyu da hamsin daga hannun masu garkuwar.

Sanarwar ta ƙara da cewa shugaban karamar hukumar Qua’an Pan, ya jaddada kudirin gwamnatin sa na inganta tsaro a yankin.

Wakilin mu ya ruwaito cewa an gabatar da mutanen da ake zargi ga manema labarai, a yayin wani taron ƙoli na tsaro da aka gudanar a barikin Koprume da ke karamar hukumar Qua’an Pan.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa masu garkuwar sun karɓi kudin fansa na Naira miliyan biyu da dubu dari biyu da hamsin.

Manship ya ƙara da cewa jami’an tsaro sun nuna ƙwarewa matuƙa, wajen kwato kudin fansar da kuma cafke mutanen da ake zargi.

A wani lamari makamancin wannan, jami’an tsaro sun kuma kama wani mutum ɗaya da ake zargi da kai hari kan matafiya a kan hanyar Juku da ke jihar Nasarawa. Ya amsa cewa suna amfani da bindigogi kirar AK47 wajen aikata laifukan su.

Shugaban karamar hukumar ya yi kira ga jami’an tsaro da su ƙara ƙaimi, wajen kama masu garkuwa da mutane da ‘yan fashi da ke addabar yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *