Labarai

Kotun soji a Najeriya za ta yanke hukunci kan wani janar bisa laifin almundahana

Saide wanda ake ƙara ya ƙi amsa laifi a kan kararrakin da aka gabatar a kansa

Wata kotun soja ta musamman a Najeriya ta sanya ranar 10 ga watan Oktoba don yanke hukunci kan shari’ar da ta yi wa wani babban hafsan soja mai mukamin manjo janar bisa tuhume-tuhumen sata da yin jabun takardu da almubazzaranci da kuma shirya maƙarƙashiya.

Manjo janar Umaru Muhammed, tsohon Manajan Darakta na kamfanin kula da kadarorin rundunar sojojin kasa ta Najeriya wato Nigerian Army Properties Limited ya gurfana a gaban kotun ne a kan tuhume-tuhume guda 18.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwati shugaban kotun, Manjo Janar James Myam, na cewa wanda ake tuhumar a ranar Laraba, ya ƙi amsa laifi a kan kararrakin da aka gabatar a kansa, inda ya gabatar da shaida biyu a kotu.

Ya ce a daya bangaren kuma mai kara wato rundunar sojin kasa ta Najeriya ta gabatar da shaida 24 a tsawon shari’ar da aka yi.

Janar James Myam ya ce tuhuma ta ɗaya an shigar da ita ne a ƙarƙashin sashe na 383, karamin sashe na kundin dokar manyan laifuka na Najeriya.

Myam ya kara da cewa, an kuma gabatar da tuhumar ne bisa sashe na 114 na dokar Sojoji Cap A20 2004.

Kotun ta ce ta samu hafsan da ake kara da laifin satar dalar Amurka miliyan 1.04 tsakanin 7 ga watan Mayun 2019, zuwa 24 ga watan Yunin 2021, lokacin da yake aiki a matsayin manajan daraktan kamfanin NAPL.

Babban alkalin kotun ya kuma ce an samu wanda ake tuhuma – da laifin bai wa wani, Manjo Usman da wani mutum wanda a halin yanzu ake neman su – umarni su dinga karbar kudi da dalar Amurka daga hannun masu jiragen ƙasa.

Sai dai Janar Myam ya ce ba a samu Janar Umaru Muhammed da laifi ba a tuhuma ta 7, wadda ta kunshi laifin hada baki don yin jabun takardu tare da wani Yusuf Abdulahi.

Haka zalika shugaban kotun ya ce an kuma samu Janar Umaru Mohammed da laifin yin jabun takardu mai alaka da tuhuma ta 8 da ta 9 a kan satar dala 430,000.

Kotun ta kuma samu wanda aka yi karar da laifin shirya makarkashiya don yin jabun takardu da sayar da kadarar kamfanin rundunar sojojin kasa a kan naira miliyan 200.

Sannan ta same shi da laifin daukar kudi naira miliyan 74 cikin wata hanya ta rashin gaskiya daga asusun kamfanin a ranar 22 ga watan Agustan 2019.

Game da tuhuma ta 14 da 15 da 16 da kuma ta 18, wadanda suka danganci babban laifin yin sama da fadi, kotun ta ce wanda aka yi zargin bai iya yin bayani a kan dukiyar da ta kai naira biliyan 2 da rabi mallakar kamfanin soja ba.

BBC Hausa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button