Labarai

Kotu tayi ɗaurin rai da rai wa wanda ya yi fyaɗe wa ƴar shekara 4 a Coci

an aikata laifin ne a cocin da ke kan titin Salau Street, ranar 29 ga watan Oktoban 2020.

 

Kotun sauraron laifuffukan fyade da cin zarafi da ke Ikeja a Jihar Legas, ta yanke wa wani mutum mai suna Ifeanyi Ndieze hukuncin daurin rai da rai saboda samun shi da laifin yi wa yarinya mai shekara hudu fyaɗe.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Abiola Soladoye, ta ce mutumin ya yi wa yarinyar fyade ne a cikin coci.

Alkalin ta ce kotun ta tabbatar da tuhumar da ake yi wa wacce ta saba da sashe na 261 na kundin manyan laifuffuka na jihar Legas na 2015.

Mai Shari’a Abiola ta ce yarinyar da aka yi wa fyaden ce ta gane mutumin da cewa ya ci mata zarafi ta hanyar cusa mata ɗan yatsa a gabanta yayin ibada a cocin.

“Daga baya an kai ta gida, amma lokacin da mahaifiyarta ta yi mata wanka, sai ta ga tana zubar da jini babu kakkautawa. A asibitin ne likitoci suka ba da shawarar a kai batun gaban ’yan sanda.

“Wannan mutumin tataccen makaeyaci ne, kuma kotu ta sane shi da aikata laifin, don haka ta yanke masa hukuncin daurin rai da rai,” in ji alkalin.

Tun da farko, lauyar gwamnati, Olufunke Adegoke, ta shaida wa kotun cewa an aikata laifin ne a cocin da ke kan titin Salau Street, ranar 29 ga watan Oktoban 2020.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button