Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar (NNPP) a zaɓen 2023 kuma jagoran ɗariƙar Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi shirin da jihar Legas ke yi na yin mulkin mallaka a yankin Arewa.
Kwankwaso, ya yi wannan zargin ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a wajen taron yaye ɗalibai na jami’ar Skyline da ke Kano, ya kuma yi ikirarin cewa Legas na da hannu wajan assasa rikicin masarautu a Jihar Kano.
Kazalika , ya kuma koka kan kalubalen da Arewa ke fuskanta da suka hadar da tabarbarewar tattalin arziki, rashin tsaro, fatara, yunwa da cututtuka iri-iri, in da ya ce lamarin bai yiwa ƙasar daɗi ba.
Daily Trust ta rawaito, Kwankwaso ya kuma ce idan aka yi duba dangane da halin da al’umma ke ciki a nan Kano da kuma Arewacin Najeriya Sarakuna sun kasance ba su da iko wajan gudanar da ayyukansu.
“Muna gani ƙarara kan yadda Legas ke nuna mulkin mallaka a wannan yanki na ƙasar nan, Yau, Legas bata barin mu mu zabi sarki da kanmu har sai ta zo ta kankane ta naɗa nasu sarkin”, in ji shi.
Kwankwaso ya kuma yi magana game da karbar haraji, in da ya ce “a Yau muna sane da cewa samarin Legas suna aiki tukuru don dora mana haraji tare da kwashe mana haraji daga Kano zuwa Legas.”
“Hatta wayoyin da muke yi ko rajista a nan Kano, ana kokarin kai duk harajin zuwa Legas”.
Tsohon gwamnan na Kano ya kuma yi tsokaci kan banbance-banbancen da ke tsakanin masu hannu da shuni da talakawa in da ya ce, “mun ga irin kokarin da wasu ke yi na ganin al’umma sun Kara talaucewa wanda acewar sa hakan ba karamar barazana bace ga al’umma”.
Don haka Kwankwaso ya yi kira ga ‘yan majalisa da suka fito daga yankin Arewacin ƙasar nan da su farka su tabbatar da cewa ba a yaudari yankin ta kowace hanya ba.
Tsadar Rayuwa: Ba Da Daɗewa Ba Abubuwa Za Su Yi Kyau -Gwamnatin Najeriya.
Babu Wata Barazana Game Da Ƙarancin Mai A Najeriya,-Manyan Dillalan Man Fetur.
Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’in Da Kwalejojin Najeriya Sun Janye Yajin Aiki
Sanata Kwankwaso, ya yi kira ga daukacin ‘yan majalisar dasu bude idanunsu don ka da su yi wani abu da zai cutar da al’ummar Arewacin Najeriya, musamman a nan Kano.
Su kuma ce “mu shaida ne kan abin da ya faru a wa’adin farko na shekarar 1999 zuwa 2000, in da aka yi wa ‘yan majalisar mu na kasa cin hanci, ta hanyar karbar makudan kudade don tallafa wa tekun kasar nan. Wannan doka ta yi matukar illa ga tattalin arzikinmu ba a nan Arewacin Najeriya kadai ba har ma da sauran jihohi baki ɗaya”.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Rikicin Siyasa Na Kara Yin Zafi A Jam`Iyyar NNPP Yayin Da Kwankwasiyya Ke Rasa Jiga-Jigai.
-
An Sake Kama Wani Mutum Da Bindigogi A Yayin Da Trump Ke Yaƙin Neman Zaɓe.
-
An Ba Wa Ganduje Wa’adin Kwanaki 7 Ya Sauka Daga Shugabancin Jam’iyyar APC.
-
A Yau Asabar Ne Ake Zaɓen Ƙananan Hukumomin Jihar Jigawa.
-
“Ku tabbatar cewa ba a sake kawo taliya mutane sun karɓa ba”-Kwankwaso.