Kamfanin Man Fetur na Ƙasa , NNPC ya tabbatar wa ƴan Najeriya cewa za a kawo karshen matsalar karancin man fetur da layukan da ake fama da su a gidajen mai daga gobe Laraba l, 31 ga Afrilu.
Olufemi Soneye, Babban Jami’in yada labarai na NNPC ne ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran na Kasa a yau Talata a Legas.
A cewar Soneye, kamfanin a halin yanzu yana samar da man fetur da ya haura lita biliyan 1.5, wanda zai iya daukar akalla kwanaki 30.
“Abin takaici, mun samu cikas na tsawon kwanaki uku wajen rabon man sakamakon matsalolin kayan aiki, wanda tun daga lokacin aka shawo kan matsalar.
“Duk da haka, kamar yadda kuka sani, shawo kan irin wannan rikice-rikice yawanci yana buƙatar ninka adadin lokaci kafin a samu daidaito ,” in ji shi.
Ya ce: “Wasu mutane suna amfani da wannan yanayin don haɓaka ribar su.
“Za share layukan mai tsakanin yau da gobe,” in ji Mista Soneye.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Hedkwatar tsaron Najeriya ta yi martani kan rahoton Amnesty.
-
An yi arangama tsakanin makiyaya da manoma a jihar Gombe.
-
Matuƙa Adaidaita Sahu za su dawo biyan haraji a Kano.
-
Emefiele ne ya mallaki unguwa mai gidaje 753 da EFCC ta ƙwace a Abuja.
-
Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta tseratar da ran mutum 4 a cikin watan Nuwamba 3 sun rasu.