Labarai
Trending

Mafarki Mara Kyau Yasa Wani Matashi Kashe Mahaifinsa Da Taɓarya.

Daga Mu’azu Abubakar Albarkawa

Yan sanda a jihar Kaduna sun ce sun kama wani matashi mai shekara 20, bisa zargin kashe mahaifinsa ta hanyar buga masa tabarya bayan zuciyarsa ta kaddara masa cewa uban na yunkurin halaka shi.

“Ya shaida mana cewa yana yin mafarke-mafarke, inda yake ganin siffar mahaifin nasa, mai kimanin shekara 50, yana zuwar masa a cikin sigar jemage,” in ji mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, kamar yadda BBC Hausa ta rawaito.

ASP Mansur Hassan ya shaida wa manema labarai cewa suna ci gaba da gudanar da bincike kan matashin da suke zargi wanda ya fito daga yankin karamar hukumar Zangon Kataf.

Ya ce zuwa yanzu ba su samu wata shaida da ke nuna cewa matashin na da wata matsalar kwakwalwa, ko kuma yana shan kayan maye.

Jami’in ‘yan sandan ya ambato matashin na cewa babu kyakkyawar alaka tsakaninsa da mahaifin, wanda ya riga mu gidan gaskiya.

‘Yan sandan sun ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da matashin mai suna David Phillips a gaban kotu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button