April 18, 2025

Majalisar Matasa ta Arewacin Najeriya ta yi Allah-wadai da hallaka mutum 51 a jihar Filato

Majalisar Matasa ta Arewacin Najeriya ta yi Allah-wadai da sabon tashe-tashen hankulla da suka barke a jihar Filato, inda ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa domin kawo karshen rikicin.

A wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata a Kaduna, majalisar ta bayyana damuwa matuka da bakin ciki kan yadda jini ke zuba ba kakkautawa, abin da ke lalata al’ummomi da kuma janyo rashin iyalai ga dubban mutane a jihar Filato.

“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa domin dakile wannan rikici. Ya zama dole hukumomi su fifita tsaron rayukka da dukiyoyin jama’a ba kawai da yin Allah-wadai da wannan ta’asa ba, har ma da tabbatar da cewa wadanda suka aikata an kama su cikin gaggawa kuma an hukunta su,” in ji Isah Abubakar, Shugaban Majalisar Matasa ta Arewa ta Najeriya.

Jaridar Punch ta yanar gizo ta ruwaito cewa, kiran da majalisar ta yi ya biyo bayan Allah-wadain da Shugaba Bola Tinubu ya yi game da hare-haren da aka kai kwanan nan a jihar Filato, wanda ya yi sanadin mutuwar sama da mutane 40.

Tinubu ya bukaci Gwamna Caleb Mutfwang da ya samu kwarin guiwa da azama na siyasa domin warware rikicin da kuma tabbatar da zaman lafiya mai dorewa.

“Wannan rikici tsakanin al’ummomi a Jihar Filato, wanda ke da tushe bisa rashin fahimtar juna tsakanin kabilu da addinai daban-daban, dole ne ya kawo karshe.” in ji Tinubu.

A gefe guda kuma, Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta bayyana ra’ayinta game da lamarin, inda ta bayyana kisan da aka yi a baya-bayan nan a matsayin barazana ga hadin kan kasa da zaman lafiya. Shugaban CAN na kasa Daniel Okoh, ya bukaci hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa wajen kama masu laifi tare da hukunta su, sannan ya bukaci gwamnati da ta kara himma wajen kare al’ummomi da hana zubar da jini.

Majalisar ta kara jaddada muhimmancin hadin kai da goyon baya tsakanin matasan Arewa domin yin kira ga zaman lafiya, da kuma bukatar daukar nauyi daga shugabanni.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *