April 18, 2025

Yan Najeriya sun tafka asarar tiriliyan 1.3 daga asusun masu zuba jari na CBEX a daga ranar Litinin

‘Yan Najeriya a dandalin sada zumunta da dama sun fara bayyana asarar da suka yi, bayan wata kafar cinikayyar kadarorin dijital da aka fi sani da CBEX ta karbe fiye da Naira tiriliyan 1.3 daga asusun masu zuba jari a ciki, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa dandalin cinikayyar dijital din ya rushe a ranar Litinin, bayan kudaden dake cikin walat ɗin masu zuba jari suka bace.

CBEX ta kuma kulle shafukkan ta na Telegram, sannan ta dage batun cire kudi yayin da ta ba da wata damar karbar $2,000 idan aka yi tantancewar $200 ko $1,000 idan aka yi tantancewar $100.

Yayin nazarin rushewar CBEX a wani taron X Space da Trending X ta shirya, wani kwararre a harkar kudin intanet da kuma tsaro, Taiwo Owolabi, ya ce bayanai sun nuna cewa kudaden an tura su zuwa wani adireshin TRX (yourself:TDqSquXBgUCLYvYC4XZgrprLK589dkhSCf), kuma jimillar kudaden da aka sace zuwa yanzu a cikin ya kai dala miliyan 847, kuma akwai yiwuwar hakan zai karu.

Owolabi ya jaddada cewa dukkan kudaden da aka saka sun tafi ne domin CBEX ba wata kafar da aka ba lasisi ba ce, kuma wadanda suka kirkiro ta sun gina wani gidan yanar gizo mai rauni da ya yi kama da na ByBit, wanda shahararren dandalin ciniki ne na gaskiya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *