Ilimi
Trending

Makarantar KTC Ta Samu Tallafin Kujeru Na Miliyan 1 Daga Ƙungiyar Tsofaffin Ɗalibai Ta 2004.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Ƙungiyar tsofaffin ɗalibai ta makarantar Kano Teaching College KTC na shekarar 2004 ta samarwa da makarantar kujerun zama na kimanin Naira milayan ɗaya.

An miƙa kujerun ne, a wani taro da ƙungiyar ta yi na bikin cika shekara 20 da kafuwar ƙungiyar wadda ake ki kira da Kano Teacher’s College Old Student Association wato KATCOSA 2004 Class a turance, a dakin taro na Rabi’u Musa Kwankwaso da ke makarantar.

Da yake ƙarin bayani ga Martaba FM Online, shugaban ƙungiyar Jamilu Abubkar Atiku, ya ce, wannan wani bangare ne na burin da suke da shi na inganta harkokin koyarwa a makarantar a matsayin su na tsofaffin ɗaliba.

“Mun shirya wannan taro ne domin sada zumunci tsakanin mu da kuma bikin cika shekara 20 da kafa ƙungiya, sannan mu miƙa gudummawar kujeru guda 50 na kimanin miliyan 1 ga makaranta, domin ƙannanmu masu tasowa su amfana, suma suga abinda suka yi, dan suma su yi wa na baya”, in ji Jamilu.

Wasu daga cikin mahalarta taron da muka zanta da sun bayyana yadda suka ji kasancewar su cikin waɗanda suka samu zuwa taron da kuma bayar da gudummawa wajen samar da kujerun, “mun yi farin ciki muna fatan yin abinda ya fi haka nan gaba”.

Malam Ɗahiru Abdullahi Yalwa, ɗaya ne da daga cikin jagororin babbar babbar ƙungiyar ta ƙasa, ya ce abinda ɗaliban ƴan shekarar 2004 suka yi ya dace domin abinda ake buƙata kenan, “daman tsakani da Allah amfanin ɗaya daga cikin ƙungiyoyin ɗalibai kenan”.

“Domin ko ba komai gwamnati abubawa sun yi mata yawa, ba za ta iya gamsar da komai ba, da irin wannan ƙungiyoyi ƙanana, taruwar da ake yi akan duba wani bangare na agaji da makarantar ke nema a kawo mata, don haka wannan ƙungiya a wajena ta cancanci ya ba wa”, a cewar Malam Jamilu.

Sai dai da yake jawabi a madadin shugaban makarantar Malam Tijjani Sani, ya ce sun gode da gudummawar kujerun to amma suna da manyan matsaloli da suke son su ƙara ƙaimi domin magance su.

Muna godiya ga wannan ƙungiya, ƙalubale baya ƙarewa, akwai ICT da ƙungiyar tsofaffin ɗalibai ta ƙasa ta gina, baya aiki kaso 70 cikin ɗari, saboda akwai wasu gyare-gyare da yake so, sannan kuma akwai wani gini wanda ke buƙatar gyara, akwai rijiyar burtsatse tana ɓuƙatar gyara, muna kira ga ko wannan chapter ko wasu a kawo gudummawa a gyara”, in ji Malam Tijjani.

Wannan shine karo na biyu da ƙungiyar ta bayar da gudummawa ga wannan tshowar makarantar tasu ta KTC.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button