Daga Sani Ibrahim Maitaya
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin ya bayar da tallafin babura 1,000 ga rundunar Ƴansandan jihar Kano, yayin gudanar da wani gagarumin biki a hedikwatar ‘yan sanda da ke Bompai.
An bayar Baburan ne da nufin inganta aikin Ƴansanda a jihar da kuma tallafa wa Yansandan Najeriya a kan ayyukan da kundun tsarin mulki ya ba su.
A cewar Barau Jibrin, tallafin na nuni ne da jajircewarsa na marawa rundunar Ƴansandan sandan Najeriya baya a kokarinsu na tabbatar da doka da oda.
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin shugaba Bola Ahmad Tinubu ta dukufa wajen yaki da duk wani nau’in rashin tsaro a faɗin ƙasar nan.
Kano Pro-pa ta nemi Gwamnatin Kano ta tsayar da ginin wasu ajujuwan karatu.
An Yi Kira Ga Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Ɓaci Kan Ta’amali Da Miyagun Kwayoyi.
Matashi Ya Kashe Kansa Sanadin Sauraron Kiɗan Gangi A Kano.
Sanatan ya yi alkawarin ci gaba da bayar da tallafi ga Ƴansandan Najeriya domin inganta ayyukansu.
Shima a nasa bangaran kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano, CP Salman Dogo Garba, ya nuna jin daɗinsa da wannan tallafin, in da ya ba da tabbacin cewa za’a yi amfani da baburan wajen inganta tsarin tsaro na jihar.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
“Kwararar masu aikata laifuka daga jihohin makwabta ne abin da ya taimaka wajen ƙalubalen tsaro”- Gwamnatin Gombe.
-
Kano da Katsina, sun zama a sahun gaba wajen matsalar rashin isassun takardun kuɗi.
-
Kamfanin Turkiyya zai fara haɓaka noman zamani a Zamfara.
-
Ƙungiyar Alkalai sun shiga yajin aikin sai baba ta gani.
-
NAFDAC ta gargaɗi masu gidajen Burodi kan amfani da Sakarin.