December 11, 2024

Kano Pro-pa ta nemi Gwamnatin Kano ta tsayar da ginin wasu ajujuwan karatu.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo.

Ƙungiyar da ke kare ayyukan Gwamnatin Kano da nagartar su wato Kano Pro-pa ta buƙaci gwamnatin jihar ta tsayar da aikin ginin ajujuwan karatu a wasu makarantu da su ke zargin rashin inganci a aikin.

Cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Alhamis, mai ɗauke da sa hannun shugabanta Alhaji Muhammad Habibu Sale Mai Lemo, ya bayyana rashin gamsuwa da aikin gina ɗakunan karatu na Kwankwasiyya Gida-Gida da ake yi a Sumaila da Gezawa.

Ƙungiyar ta gano rashin ingancin aikin ne bayan wata ziyara da suka kai a ƙananan hukumomin bisa umarnin gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, kamar da sanarwar ta bayyana.

“Muna kira ga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kano da ta dakatar da aikin da ‘Yan kwangilar ke yi saboda rashin ingancin sa da kuma rashin amfani da kayan aiki masu inganci, har sai an kammala cikakken bincike”, in Sale Mailemo.

Ya kuma bayyana damuwarsa ganin mafi yawan yan kwangilar yan asalin ƙananan hukumomin ne kuma ƴaƴansu da na ƴan uwansu ake sa ran su yi amfani da gine-ginen “don haka muna jaddada bukatar gaggawar ɗaukar mataki daga gwamnatin jiha don gyara lamarin”, in ji shi.

Kwankwaso Ya Yi Zargin Ana Neman Yi Musu Dole Daga Lagos A Harkar Masarautun Kano.

Matashi Ya Kashe Kansa Sanadin Sauraron Kiɗan Gangi A Kano.

Gwamnatin Kano Za Ta Fara Tantance Baƙi Ƴan Kasashen Waje Da Ke Jihar.

Sai dai kuma Alhaji Muhammad Habibu Sale Mai Lemo, ya yabawa ƴan kwangiloli da ake gudanar da aikin gina Ajujuwa na Kwankwasiyya Gida-Gida a ƙananan hukumomin Tofa, Wudil, Garko, Warawa da Bichi saboda ingancin aikinsu.

Ya bukace su da su ci gaba da gudanar da aiki mai kyau tare da bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa a kwangilar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *