Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Kamfanin matatar mai ta Dangote ya bayyana cewa ya ƙulla yarjejeniya da kamfanonin Heyden Petroleum da Ardova Plc don tabbatar da samar da man fetur a farashi mai sauƙi ga ƴan Najeriya.
Daily Nigerian ta rawaito, cikin wata sanarwa da matatar man ta Dangote ta fitar a jiya Alhamis, ta ce kamfanonin biyu sun shiga yarjejeniya ta sayan mai da yawa daga matatar Dangote, tare da samun tallafi daga shirin sayen ɗanyen mai da Naira da Shugaba Bola Tinubu ya kaddamar.
“Wannan mataki na dabarun kasuwanci an tsara shi ne don tabbatar da wadatar dangogin mai a farashi mai rahusa, daidaita kasuwar man fetur ta ƙasa, tare da inganta tsaro wajen samar da makamashi ga masu amfani,” inji sanarwar.
Matatar Dangote haɗin gwiwa da kamfanin mai na MRS za su sayar da fetur a kan N935 duk lita.
Nan da Makwanni Ƴan Najeriya za su yi murmushi a 2025 – Shettima.
Bankin Duniya ya ce har yanzu Najeriya ba ta kama hanyar yaƙi da rashawa ba.
Dangote ya ce wannan ci gaban ya biyo bayan misalin da kamfanin MRS ya kafa, wanda ya riga ya shiga irin wannan yarjejeniya da Dangote .
Sakamakon haka, MRS ya rage farashin mai zuwa Naira 935 kowace lita a duk gidajen manfetur dinsa a faɗin ƙasa, don magance matsalar bambancin farashi tsakanin jihohi.Dangote ya ƙulla yarjejeniya da kamfanoni biyu don karya farashin man fetur.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnan Kano ya amince da murabus ɗin Kwamishinan Ma’aikatar Bibiya da tabbatar da Nagartar Aiki.
-
Gwamna Zulum zai saka tallafin man fetur ga manoman yankin da rikicin Boka Haram ya shafa.
-
Sarakunan da Fintiri ya naɗa bayan ƙirƙirar masarautu 7 a jihar Adamawa.
-
Jami’an tsaro sun ragargaza Lakurawa a jihar Kebbi.
-
Me Shamsiyya ta aikata `Yansanda Kano su ka kama ta da abokanta?