Ana nuna damuwa cewa har yanzu gwamnoni Ashiru da biyu sun kaucewa biyan sabon albashin mafi ƙanƙanta na Naira 70,000, da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba wa hannu ya zama doka tun ranar Litinin 29 ga watan Yuli 2024.
Yayin da yawancin shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago ke kan daukar matakin da ya kamata su ɗauka dangane da ƙin aiwatar da sabon albashin da wasu gwamnatoci ke yi.
Duk da cewa shugabannin ƙwadago sun sha alwashin durƙusar da harkokin duk wata jiha da ta ƙi biyan albashin da aka kayyade, musamman a wannan lokaci da tsadar rayuwa ke ƙaruwa wanda ke mayar da N70,000 kamar ba komai, har yanzu suna cikin shawarwarin matakin da ya fi dacewa su ɗauka.
Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC) Kwamared Joe Ajaero, ya yi gargaɗi kan duk wani abu da zai iya haifar da shiga yajin aiki.
A wata hira da jaridar LEADERSHIP, Ajaero ya jaddada cewa “Albashin mafi ƙanƙanta na yanzu na Naira 70,000 yana rasa ƙima kullum, kuma nan ba da daɗewa ba, ba zai iya siyan toilet paper ba”
A wata hira daban, Shugaban Ƙungiyar Ma’aikatan Abinci, Giya da Taba na Ƙasa (NUFBTE), Kwamared Garba Ibrahim, ya ce babu wata hujja da gwamnoni ke da ita na ƙin aiwatar da sabon albashi.
“Babu wata jiha da ba ta da arziki da zai hana ta biyan albashin da aka kayyade, wannan yunkuri ne na danne ma’aikata da sa su cikin talauci.
“Wannan yana da illa mai girma saboda yana barazana ga kyakkyawar alaƙar ma’aikata da kuma take haƙƙin su bisa ka’idojin ƙasa da ƙasa na kwadago,” in ji Ibrahim.
Sai dai Ibrahim ya bayyana damuwa kan ƙarfafa aiwatar da biyan, duba da cewa wasu jihohi ba sa da ƙarfin kuɗin da zai ɗora su akan wannan sabon tsarin biyan albashi.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya