Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Jubril Barau, da Ministan Noma da samar da Abinci Sanata Abubakar Kyari, sun bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Bola Tinubu ke aiwatarwa a fannin noma, suna haifar da sakamako mai kyau.
Sun yi wannan bayani ne a wajen wani shirin tallafi na noma da ci gaban bil’adama da Sanata mai wakiltar Kwara ta Tsakiya Salihu Mustapha ya shirya a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Sanata Barau ya ce noma da ci gaban bil’adama su ne ginshikan ci gaban kowace kasa.
A wajen taron da aka gudanar a harabar Hukumar Raya Kogin Niger (Lower Niger River Basin Development Authority) mai taken “Alubarika 1.0 Agricultural and Human Capital Development Empowerment Programme”, Sanata Mustapha ya raba kayan tallafi da kayan aiki ga fiye da mutum 2,500 daga mazabar sa a Ilorin.
Barau ya ce: “Babu bukatar bata lokaci wajen bayani kan muhimmancin noma ga kowace al’umma. Noma shi ne ginshikin rayuwa, domin ba tare da abinci ba, babu rayuwa, Wannan ne dalilin da ya sa Majalisar Dattawa ta naɗa Mustapha a matsayin Shugaban Kwamitin Noma.
A nasa jawabin, Minista Kyari ya ce shirye-shiryen da Shugaba Tinubu ke aiwatarwa a bangaren samar da abinci suna yin tasiri.
Ya ce: “Mun ga cewa abinci yana wadatuwa, kuma farashin sa yana raguwa a hankali.
Tun da farko Sanata Mustapha ya bayyana cewa shirin tallafin nasa yana da alaka da ajandar shugaba Tinubu na Renewed Hope, yana mai cewa: “Mun dauki lokaci muna horar da mutane kan gyara da kula Fanal-fanal (solar panels).”
Ya kara da cewa wannan shiri na tallafawa mata ‘yan kasuwa, manoma, masu sana’o’in hannu da kungiyoyin yan kasuwa domin su zama masu dogaro da kansu.