Daga Fatima Suleiman Shu’aibu
Harin sama da jiragen yakin Sojin Sama na Najeriya suka kai sun hallaka ‘yan ta’adda da dama tare da lalata wata motar yaki a Kukawa, jihar Borno.
An kashe ‘yan ta’addan ne a hare-hare guda biyu daban-daban da aka kai a ranar 25 ga Nuwamba.
Kakakin rundunar sojan, Air Commodore Olusola Akinboyewa, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, 27 ga Nuwamba.
Akinboyewa ya ce: “A harin farko, jiragen yakin NAF sun lalata wata motar yaki sannan suka kashe ‘yan ta’adda da dama. Harin na biyu kuma domin bayar da kariya ta sama don dakile wani hari da aka kai kan sojojin kasa.
“Harin farko ya fara ne da sahihan bayanai kan inda wata motar yaki ta ‘yan ta’adda take, kimanin kilomita 5 a yamma da Kukawa. Jiragen yakin NAF sun yi saurin daukar mataki, inda suka kai farmaki kan wurin tare da lalata motar yakin da kuma rage karfin ‘yan ta’addan.”
Ƴarsanda ta yi barazanar kashe kanta da ƴaƴanta.
Kutu ta ɗaure likitan bogi da ya yi shekaru 10 ya na aiki a Abuja.
An gano shinkafar da Tinubu ya bayar a raba ana canza musu buhu a Kano.
A harin na biyu kuwa, bangaren Sama na Operation Hadin Kai (OPHK) sun amsa kiran gaggawa daga sojojin kasa a Kukawa, inda aka kai musu farmaki mai tsanani daga ‘yan ta’adda a kan babura.
Jiragen yakin NAF sun yi saurin daukar mataki, inda suka kai farmaki kan ‘yan ta’addan a wurare daban-daban.
Harin ya hallaka da dama daga cikin ‘yan ta’addan, yayin da sojojin kasa suka kwato fiye da babura 20 da aka bari.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
“Kwararar masu aikata laifuka daga jihohin makwabta ne abin da ya taimaka wajen ƙalubalen tsaro”- Gwamnatin Gombe.
-
Kano da Katsina, sun zama a sahun gaba wajen matsalar rashin isassun takardun kuɗi.
-
Kamfanin Turkiyya zai fara haɓaka noman zamani a Zamfara.
-
Ƙungiyar Alkalai sun shiga yajin aikin sai baba ta gani.
-
NAFDAC ta gargaɗi masu gidajen Burodi kan amfani da Sakarin.