Labarai
Trending

Sojin Saman Najeriya Sun Kashe Ƴan Bindiga A Dazukan Kaduna Da Zamfara.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

A wasu hare-hare da rundunar sojin saman Najeriya suka kaddamar sun kashe tarin ƴan ta’addda a Kaduna da Zamfara.

RFI ta rawaito, Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojin saman, Edward Gabkwet ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi a Abuja.

Mr Gabkwet ya ce rundunar musamman ta Operation Whirl Punch ta ci gaba da aikinta na gano sansanin ƴan ta’addda tare da tarwatsa su.

Ya ce bayanan sirri sun bayyana cewa ƴan ta’addan da ke addabar al’umma ta wajen kisa da yin garkuwa da su a ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja su na zaune ne a jihar Kaduna.

Allah ya yi wa Sarkin Ningi Alhaji Yanusa Ɗanyaya rasuwa.

Iyalan Sarkin Kano Ado Sun Ƙaryata Alaƙa Da Zainab Wadda Take Iƙrarin Ita Ɗiyar Sarkin ce.

A cewarsa, karin bayanan sirri sun nuna cewa waɗannan ƴan ta’adda su na ƙaura daga dajin Allawa na jihar Neja zuwa dajin Malum na ƙaramar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Nasarar sojin na zuwa ne yayin da bindiga ke ci gaba da cin karen su ba babbaka a jihohin Arewacin Najeriya, in da a makon da ya gabata suka kashe Sarki bayan sun yi garkuwa da shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button