April 18, 2025

Warning: sprintf(): Too few arguments in /home/martabaf/public_html/wp-content/themes/elegant-magazine/lib/breadcrumbs/breadcrumbs.php on line 254

Tsohon ɗan wasan Najeriya Utaka ya buƙataci ƴan wasan Super Eagles su jajarice dan kai wa ga buga Kofin Duniya

Tsohon dan wasan Super Eagles na Najeriya John Utaka, ya bukaci ‘yan wasan kungiyar da su ci gaba da nuna jajircewa da kwarin gwiwa, wajen neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2026.

A halin yanzu kasar Afirka ta Kudu ce ke kan gaba a rukunin C da maki 13, yayin da Najeriya ke matsayi na hudu da maki 7, maki daya ne kacal ke raba ta da Rwanda da Benin wadanda ke da maki 8 bayan zagaye shidda na wasannin.

A wata hira da ya yi da Brila FM, Utaka ya jaddada bukatar ‘yan wasan da su nuna karin jajircewa da mayar da hankali domin cimma burin zuwa gasar cin kofin duniya.

“Da irin baiwar da muke da ita, bai kamata mu kasance a wannan matsayi ba. Dole ne mu hade mu mayar da hankali wajen cika burin zuwa gasar cin kofin duniya. Dole ne mu nuna irin azama da jajircewar da sauran kasashe ke nunawa”.

“A cikin kwallon kafa, komai na iya faruwa. Bai kamata mu karaya ba. Ina da yakinin cewa za mu iya samun tikitin, amma hakan yana da nasaba da yadda za mu fuskanci wasannin da ke tafe.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *