Tsohon mai horar da ƙungiyar kwallon ƙafar Najeriya Super Eagles Christian Chukwu ya mutu a safiyar Yau Asabar ya na da shekaru 74 a Duniya.
Sai dai kawo yanzu ba a tabbatar da musabbin mutuwar kocin ba, labarin mutuwar kocin ya jefa masoya kwallon kafa a Najeriya cikin jimamin shin mai horarwar .
Chukwu da ake kira da ”Ciyaman” ya kasance jigo na musamman a bangaren tamola a Najeriya, hasali ma a yayin da yake kan ganiyarsa na buga wasa da kuma yayin gudanar da aikinsa na Horarwa.
Ya rike matsayin Jagoran tawagar Yan wasa (Captain) na kungiyar Super Eagles, wanda ya janyo masa martaba daga masoya kwallon kafa, bisa irin kwarewarsa da kuma jajircewa yayin buga wasanni .
A shekarar 2021 an taɓa yaɗa jita-jitar mutuwarsa a kafafen sada zumunta, wanda ya karaɗe kafafen a wancan lokacin.
In da daga bisani labarin ya kasance na kanzo kurege da ya haddasa ce-ce-kuce , bayan bikin zagayowar ranar haihuwarsa na cikarsa shekaru 70 a Duniya , A ranar 4 watan Junairu.
“Na yi matukar jin takaicin labarin da aka yada na cewa na mutu, mutane da dama sun kira ni daga ƙasashen Duniya daban-daban yayin da aka yada wannan labarin . Ina cigaba da bincike kan asalin inda labarin ya fito, a cewarsa .
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya