Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja Nyesom Wike, ya ce Gwamnan jihar Rivers da aka dakatar Siminalayi Fubara, bai nemi gafarar sa ba balantana ya yi la’akari da yi masa afuwa.
A cewar sa, domin a samu gafara, dole ne wanda ya aikata kuskure ya amince da kuskuren sa sannan ya nemi afuwa.
Ministan ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai Lere Olayinka, yana mayar da martani ne kan kiran da tsohon shugaban gungun yankin Niger Delta Cif Government Ekpemupolo (wanda aka fi sani da Tompolo) ya yi, inda ya bukaci Wike da ya yafe wa Fubara.
Tompolo yayin da yake magana kan rikicin siyasa a jihar Rivers a wata sanarwa da ya fitar kwanan nan, ya jaddada muhimmancin hakuri da haɗin kai, tare da roƙon Wike da ya ajiye fushin sa domin amfanin jama’a.
Ya ce: “Kamar yadda ba zan yarda ɗana ya yi tawaye ba, haka kuma ba zan ƙara haifar da matsala ba. Wike yana cikin fushi, amma dole ne ya sauke fushin sa domin amfanin kowa. Za mu tattauna mu warware matsalolin da suka rage, sannan Fubara zai dawo kan kujerarsa.”
Da aka nemi jin ta bakin sa kan kiran da Tompolo ya yi, Wike ta bakin mai magana da yawun sa ya ce “Babu wani laifi. Ana magana ne kan neman afuwa idan mutum ya cutar da kai kai tsaye. A matsayin mu na Kiristoci, bari mu ɗauka cewa Fubara ya cutar da minista, shin ana yafe wa mutum wanda bai zo gare ka ya nemi gafara ba?”
Olayinka ya jaddada cewa dole sai wanda ya yi kuskure ya gane cewa ya yi, sannan ya nemi afuwa. Ya ƙara da cewa: “Mutumin da ya yi maka laifi dole ne ya yarda a ransa cewa ya yi kuskure. Mu ɗauka cewa Fubara ya yi wa minista laifi, shin ya zo ya nemi afuwa? Ba ma cewa akwai laifi da ya kamata a gafarta, amma har yanzu bai ma zo ya nemi gafara ba.”
A cewar sa, Wike bai zargi Fubara da wani laifi na kai tsaye ba, sai dai kawai yana neman a bi ka’idojin shugabanci.
Ya ƙara tambayar dalilin da ya sa Fubara ya canza ra’ayi game da Wike, yana cewa Fubara da kansa ya yi aiki da Wike da ƙwarin guiwa a baya.