Kasuwanci
Trending

Za Mu Kawo Ci Gaba A Kasuwar Kurna Babban Layi-Malikawa.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

Zaɓaɓɓen shugaban kasuwar Kurna Babban Layi da ke ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano, Alhaji Mustapha U Malikawa, ya sha alwashin samar da ci gaba a kasuwar, wadda ta haura shakara 40.

Malikawa, ya bayyana haka ne a lokacin da ya ke jawabi a wajen taron rantsar da shi da sauran shugabannin kasuwar da aka yi a safiyar ranar Lahadin nan.

“Babu shakka akwai tarin ƙalubale sosai ta ɓangarori da dama musamman abin da ya shafi tsaro, za mu yi aiki tuƙuru dan kawo gyara”, in shi.

Ya kuma ce, za su bi duk wata hanya dan samo wa yan kasuwar ci gaba da kawo musu duk wani tsari da zai taimaka wajen haɓaka kasuwancin su, tun daga gwamnatin Najeriya zuwa ta Kano.

Barrister Abubakar Hussaini Maƙari, shine wanda ya ba wa shugabannin rantsuwa, ya hore su da su zama masu biyayya ga kundin tsarin mulkin Najeriya da na kasuwar, tare da yin aiki tuƙuru domin tabbatar da adalci da zaman lafiyar kasuwar, da kuma haɗa kai wajen tabbatar ci gaba domin sauke nauyin da Allah ya ɗora musu.

Taron wanda ya samu halartar jami’an gwamnati da masu sarautar gargajiya, ƴan kasuwa da kuma ƙungiyoyi, ya gudana ne a tsakiyar kasuwar ta Kurna Babban Layi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button