Tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Zamfara Ibrahim Dosara, ya karyata ikirarin da gwamnan jihar Dauda Lawal ya yi cewa, ya tarar da naira miliyan 4 kacal a asusun gwamnati.
Dosara ya mayar da martani ne ga wata hira da Lawal ya yi da gidan talabijin na Arise a ranar 14 ga watan Afrilu, inda ya bayyana cewa ya samu jihar cikin halin ruɗani lokacin da ya karɓi mulki daga hannun tsohon gwamna Bello Matawalle, wanda yanzu shine Ƙaramin ministan Harkokin Tsaro na ƙasa.
A lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Kaduna ranar Litinin, Dosara ya bayyana wannan ikirari a matsayin “ƙarya tsagwaron ta”.
“Mun ji ƙarfin hali saboda halin da wannan batu ya kawo, inda aka yi zargin da ba dai-dai ba kuma da gangan, a kan gwamnatin mu ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan jihar Zamfara Mai Girma Bello Muhammad Matawalle, cewa an aikata laifukka a lokacin mulkin sa, kamar yadda gwamna mai ci yanzu, Dr. Dauda Lawal ya bayyana a cikin hirar da ya yi Arise TV ranar Litinin 14 ga watan Afrilu 2025.”
“Wannan ƙarya ce tsagwaron ta; domin kawar da duk wani shakku, tsohon gwamnan ya bar waɗannan kuɗaɗen a asusun gwamnati a ranar da ya mika mulki ga gwamna mai ci Dr. Dauda Lawal: Naira biliyan 14 daga ribar lamuni, Naira biliyan 2 da milyan dari shidda daga kuɗaɗen Bankin Duniya, Naira biliyan 6 da miliyan dari ukku na tallafin hukumar UBE, da Naira biliyan 2 da miliyan dari bakwai na NG Cares daga Bankin Duniya, wanda ya samar da ribar Naira biliyan 42 ga gwamnatin Lawal,” in ji Dosara.
Ya ƙara da cewa tsohon gwamnan ya bar bashi na albashin watanni ukku ne kacal, saboda ƙarancin kuɗaɗen da ake samu a jihar.
“Ban san ko muna da albashin rabin wata a tsarin aikin gwamnati ba,” in ji shi.
Ya kara da cewa “Don a tabbatarwa, gwamnatin ta bar bashi na albashin watanni ukku ne, domin ko kafin Dr. Dauda Lawal ya hau mulki, ya riga ya yi barazanar cire hulɗa da duk wasu bankuna da suke da yarjejeniyar kuɗi da gwamnatin da ke barin gado.”