Daga Suleman Ibrahim Modibbo
Rundunar Ƴansandan jihar Bauchi ta tabbatar da kama wasu mutane uku da ake zargi da hannu a wani mummunan lamari da ya shafi haɗa kai wajen aikata laifi, zina, zubar da ciki da kuma kisan kai.
A cewar sanarwar da Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar, lamarin ya faru ne sama da watanni hudu da suka wuce a garin Misau.
Wadanda ake zargin sune: Usman Umar, mai shekara 22 mazaunin unguwar Fawari, Misau da Sallau Ayuba, mai shekara 21 daga unguwar Lariski, Misau sai kuma Abubakar Mohammed, mai shekara 35 daga Misau, kuma ɗalibi a shekara ta biyu a Kwalejin A.D Rufai ta Karatun Addini da Shari’a.
Sanarwar ta ce, “bisa ga bincike, Usman da Sallau sun yaudari wata budurwa mai shekaru 18 (sunanta an boye), in da suka yi lalata da ita a lokuta daban-daban, ciki har da a wani otal da ake kira Mahmood Lodge da ke cikin garin Misau., wannan ya haifar da ɗaukar ciki”
“Da suka fahimci ta dauki ciki, sai suka gayyato Abubakar Mohammed kuma suka ba shi naira 40,000 domin ya mata allurar da za ta zubar da cikin. Bayan an yi mata allurar, budurwar ta suma kuma ta kamu da matsananciyar rashin lafiya. Daga bisani aka garzaya da ita Asibitin Gwamnati na Misau, daga nan aka mayar da ita Asibitin Koyarwa na Tarayya (FMC) da ke Azare”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Wakil ya ƙara da cewa, “sai dai cikin takaici, an tabbatar da rasuwarta a yayin da take karbar kulawa a asibitin”
“Bayan samun rahoton, rundunar ‘yan sanda ta kama waɗanda ake zargin kuma sun amsa laifinsu. Sannan sun ambaci wasu da suka hada kai da su a cikin lamarin, da suka haɗar da Alkali Kawu, Maule Mai Ride sai kuma Mai Tumatur, Danguli, Yakubu da kuma wani da aka kira da Kura (ma’aikacin gwamnati)”, in ji shi.
Ƴansanda sun kuma ce akwai ƙarin wasu mutum huɗu da ake ci gaba da bincike a kansu a ofishin Ƴansanda na Misau.
Rundunar ta tabbatar da aniyar ta na ganin adalci ya tabbata ga marigayiyar, kuma za a gurfanar da wadanda ake zargi a kotu da zarar bincike ya kammala.