Labarai
Trending

A Karon Farko Emefiele Ya Kwana A Gidansa Bayan Shafe Kwanaki 151 A Tsare.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

rahotanni a Najeriya sun ce a jiya ne tsohon gwamnan babban bankin Najeriya, CBN, Godwin Emefiele, ya isa gidansa da ke Abuja, bayan da wata babbar kotun Abuja ta bayar da belinsa.

BBC ta ce Emefiele ya shafe “kwanaki 151 a hannun jami’an tsaro”.

Babbar kotun tarayyar Najeriya da ke zamanta a Maitama ta bayar da umarnin a sake shi daga gidan yari, duk da rashin amincewar da babban lauyan gwamnatin tarayya, AGF, da hukumar yaki da cin-hanci da rashawa EFCC suka yi.

Babu Wanda Zai Daina Karɓar Kuɗaɗen Naira Da CBN Ya Samar- Babban Bankin Najeriya.

Kotun, a hukuncin da mai shari’a Olukayode Adeniyi ya yanke, ta bayar da umarnin a saki tsohon gwamnan babban bankin ga lauyoyinsa, duk da cewa ta umarce shi da ya miƙa dukkan takardun tafiye-tafiyen sa na kasashen waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button