Labarai
Trending

KAROTA Za Ta Tsare Wasu Jami'inta Kan Zargin Yawan Karɓar Kuɗaɗe A Hannun Direbobi.

Daga Suleman Ibrahim Modibbo

A jihar Kano da ke Najeriya, hukumar KAROTA mai kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Jihar ta ce ya zama wajibi ta ɗauki matakin fitar da ɓata-garin cikinta domin inganta ayyukan hukumar.

Cikin wata sanarwa da KAROTA ta fitar a ranar Alhamis mai ɗauke da sa hannun kakakin ta Nabulusi Abubakar Kofar Na’isa, shugaban kukumar KAROTA Engr. Faisal Mahmud Kabir, ya bayar da umarnin tsare wasu Jami’in KAROTA waɗanda ake zargin su da matsawa direbobin mota da karɓe-karɓen kudi a wajen su.

“Hukumar ba za ta zuba ido ta bari a sauke tsarin da aka kafa hukumar a kai ba, a don haka ya zama wajibi a hukunta duk wanda aka samu da sauya salon aikin hukumar”, in ji sanarwar.

Shugaban hukumar ya ja hankalin direbobin mota da su guji bawa Jami’in hukumar ta KAROTA cin-hanci domin baya daga cikin manufar kafa hukumar, wanda ya ce, “abinda ake bukata a wajen kowanne direba shi ne ya tabbatar ya mallaki dukkan takardun toki kafin ya hau kan titi, da kuma bin dokokin hanya a lokacin da ake tokin”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button