Kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin Mai shari’a Okon Abang, a ranar Juma’a sun dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke a ranar 10 ga watan Janairu, wanda ya soke wancan hukunci na Kotun Jihar Kano da ya rusa naɗin Sanusi na II, bisa dalilin rashin hurumin yin hakan.
Hukuncin da Mai shari’a Gabriel Kolawole ya yanke ya nuna cewa, soke naɗin Sanusi na II ba ya kan ka’ida, don haka ya umarci a mayar da ƙarar zuwa Babbar Kotun Jihar Kano.
Duk da haka, yayin da yake yanke hukunci kan sabbin bukatu masu lamba CA/KN/27M/2025 da CA/KN/28M/2025, Kotun Ɗaukaka Ƙara ta amince da bukatun da ke neman dakatar da aiwatar da hukuncin da aka yanke har sai an kammala ɗaukaka ƙara a gaban Kotun Ƙoli.
“Doka ta tanadi hakan. Kotun na da hakkin amfani da ikonta bisa adalci da kuma don tabbatar da gaskiya,” in ji shi, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.
Mai shari’a Abang ya kuma bayyana cewa dole ne a kiyaye batun da ke gaban kotu, saboda mai ɗaukaka ƙarar ya rike sarauta na tsawon shekaru biyar kafin a tube shi, don haka ya na da haƙƙi kariya.
A ranar 10 ga watan Janairu, Mai shari’a Kolawole yayin da yake soke hukuncin da ya rushe nadin Sanusi na II, ya bayyana cewa lamarin ya na da alaƙa da sarauta, don haka ya kamata a yanke hukunci a Babbar Kotun Jihar Kano a maimakon Babbar Kotun Tarayya, wanda ya ce yin hakan babban kuskure ne.
A baya, a ranar 20 ga watan Yuni 2024, Babbar Kotun Tarayya da ke Kano karkashin jagorancin Mai shari’a Abubakar Liman, ta soke dokar da gwamnatin jihar Kano ta kafa wato Kano Emirates Council (Repeal) Law 2024, wacce ta mayar da Muhammadu Sanusi na II a matsayin Sarki na 16.
LABARAI MASU ALA'KA DA JUNA
-
Gwamnatin Kano ta tabbatar da za ta yi adalci da sauraron ƙorafe-ƙorafen al’ummar da aikin magance zai zayar ƙasa zai shafa a Bulbula tare da biyan diyya
-
Buba Galadima ya ƙaryata batun komawar Kwankwaso APC da Ganduje ya yi
-
NSCDC ta tura Jami’ai 415 a Zamfara don tabbatar da tsaro lokacin bukukuwan Easter
-
Ƴansandan Najeriya Najeriya sun cafke mutum biyu kan rikicin baya-bayan nan da ya afku a jihar Filato
-
Shugaba Tinubu ya ƙaddamar da sabon kwamitin ƙidaya